in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libya ta alkawarta gudanar da bincike game da zargin muzgunawa bakin haure
2018-01-23 09:48:47 cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Libya ta umarci sassan tsaro da na shari'ar kasar, da su binciki gaskiyar wani faifan bidiyo da yake yawo ta kafofin sada zumunta, mai daure da wasu mutane na azaftar da wasu da aka nuna bakin haure ne.

Ma'aikatar ta kuma yi kira ga sassan kasa da kasa da su tallafawa jami'an tsaron kasar ta Libya, wajen dakile ayyukan muggan kungiyoyi dake karya dokokin kasar.

Shi dai faifan bidiyon na baya bayan nan ya nuna yadda wasu mutane ke azaftar da wasu, da ake zaton bakin haure ne dake shiga kasar ta Libya a kan hanyar su ta tsallakawa nahiyar Turai.

A baya ma dai gidan talabijin na CNN ya wallafa wani rahoto dake nuna yadda ake sayar da 'yan ci rani a sassa daban daban na kasar ta Libya, inda aka nuna ana sayar da bakin hauren da kudin da bai wuce dalar Amurka 400 ba.

Wannan faifai dai ya haifar da matukar damuwa tare da tir daga kasashen duniya daban daban, game da yadda cinikin bayi ke kokarin dawowa, a daya hannun kuma mahukuntan Libya sun sha alwashin gudanar da bincike kan hakan.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China