in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cafke mutane 61 da ake zargi da kai harin filin jirgin saman Tripoli
2018-01-22 09:30:40 cri

Dakarun rundunar tsaron kasar Libiya sun ce, sun cafke mayaka masu dauke da makamai 61, bisa zargin su da hannu a harin kwanan baya da aka kai filin jirgin sama na M'etiga dake birnin Tripoli.

Wata sanarwa ta bayyana cewa, baya ga filin jirgin saman, maharan sun kuma kaiwa gidan yari dake daura da wurin farmaki. Yanzu haka dai ana can ana gudanar da bincike kan mutanen da aka kama, tuni kuma aka saki 6 daga cikin su.

A Litinin din farkon makon jiya ne fada ya barke a filin jirgin saman na Tripoli, tsakanin dakarun masu dauke da makamai da jami'an tsaron kasar, lamarin da ya haddasa kisan mutane 21, aka kuma raunata wasu 69 ciki hadda fararen hula.

Bayan aukuwar tashin hankalin, gwamnatin Libiya mai samun goyon bayan MDD ta fitar da wata sanarwa, wadda ta yi Allah wadai da farmakin, tana mai dangatashi da wani yunkuri na kubutar da mayakan IS da na al-Qaida da sauran 'yan ta'adda dake tsare a gidan yari.

An dai sake bude filin jirgin saman kasar dake birnin Tripoli a ranar Asabar din karshen mako.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China