in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
NAPTIP: Ana tsare da 'yan Najeriya 25,000 a sansanonin sayar da bayi a Libya
2017-12-20 08:52:18 cri

Hukumar yaki da safarar bil-Adam ta Najeriya (NAPTIP) ta ce, ana tsare da 'yan kasar sama da 25,000 a sansanonin sayar da bayi da cin zarafin mata a kasar Libya.

Shugabar hukumar Julie Okah-Donli ce ta bayyana ta bayyana hakan, tana mai cewa, ya zuwa yanzu, hukumarta tare da taimakon hukumar kula da kaurar jama'a ta duniya (IOM) da kungiyar tarayyar Turai (EU)sun yi nasarar kwashe 'yan kasar kimanin 5,000 zuwa gida.

A cewar jami'ar, lamarin da ke faruwa na sake dawo da cinikin bayi, abu ne mai tayar da hankali wanda kuma ke bukatar kulawar kasashen duniya.

Ta ce, Najeriya za ta ci gaba ta bijiro batun safarar bil-Adama a tarukan kasa da kasa daban-daban, haka kuma mahukuntan kasar za su yi kokarin daukar matakan da suka dace na magance kaurar bakin haure ba bisa ka'ida ba.

A farkon watan Disamban wannan shekarar ce, gwamnatin Najeriyar ta ce ta gano 'yan kasarta kimanin 2,778 da ake tsare da su a sansanoni daban-daban a kasar ta Libya. Wannan ya sa mahukuntan Najeriyar suka lashin takwabin ganin sun dawo da 'yan kasar nata zuwa gida. A hannu guda ofishin jakadancin Najeriyar dake Libya zai ci gaba da tattaunawa da gwamnatin Libya da sauran masu ruwa da tsaki wajen ganin an dawo da 'yan Najeriyar da suka makale a kasar ta Libya zuwa gida.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China