in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukuntan Libya tsagin gabashi sun amince da gudanar da babban zabe
2017-12-28 09:14:41 cri

Kakakin hukumar gudanarwa kasar Libya mai helkwata a gabashin kasar Ahmad Mismari, ya ce bangaren su ya amince da a gudanar da babban zaben kasa kafin karshen shekara ta 2018 dake tafe.

Yayin wani taron manema labarai da ya gudana a birnin Benghazi, Mismari ya ce, akwai bukatar MDD, da kungiyar kasashen Larabawa su sanya ido ga gudanar zaben domin tabbatar da gaskiya da adalci.

A watan Satumbar da ya gabata ne dai jagoran tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD mai aiki a Libya Ghassan Salame, ya ba da shawarar daukar matakan warware takaddamar siyasar da ta dabaibaye kasar.

Shawarar dai ta kunshi sauya wasu sassa na yarjejeniyar siyasar da MDD ke marawa baya, tare da gudanar da babban zaben kasar kafin karshen shekarar 2018.

Tawagar tare da hukumar zaben kasar ta Libya, sun kuma sanya hannu kan wata yarjejeniya a watan Disambar nan, wadda ta kunshi tsare tsare da fasahohin da za a yi amfani da su, wajen tabbatar da nasarar zaben dake tafe.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China