A cewar jami'in, kokarin kiyaye zaman lafiya a kasar Afghanistan, ya shafi moriyar jama'ar kasar, da burin samun ci gaba, da walwala a yankin da kasar ke ciki. Ya ce, kasar Sin ta yaba wa gwamnatin kasar Afghanistan, kan yadda take kokarin tabbatar da zaman karko, da neman samun masalaha tsakanin al'umma. Tana kuma martaba muhimmiyar rawar da kasashen dake makwabtaka da Afghanistan suke takawa, a kokarin daidaita al'amura a kasar.
A sa'i daya kuma, a cewar jami'in na kasar Sin, kasar sa na kira ga gamayyar kasa da kasa, da su goyi bayan Afghanistan, ganin yadda kasar ke fuskantar kalubaloli a fannoni daban daban.(Bello Wang)