Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, da jagoran shirin majalissar dake tallafawa ayyukan jin kai a Afghanistan ko UNAMA a takaice Tadamichi Yamamoto, sun yi Allah wadai da harin da aka kaiwa otal din Intercontinental a birnin Kabul, fadar mulkin Afghan.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi, Mr. Guterres ya gabatar da sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su, tare da fatan samun sauki cikin sauri ga wadanda suka jikkata.
A kalla mutane 18 ne suka rasu, ciki hadda 'yan kasashen waje 14 a harin na birnin Kabul. An kuma ce dukkanin maharan 5 sun rasa rayukan su yayin musayar wuta da dakarun tsaron kasar. An dai shafe sa'o'i 12 ana dauki ba dadi kafin a kai ga kawo karshen mamayar maharan.
Tuni dai kungiyar Taliban ta dauki alhakin kaddamar da harin, tana mai cewa, maharan su 5 sun yiwa otal din tsinke, a wani mataki na kaddamar da hari kan jami'an gwamnati da baki 'yan kasashen waje dake cikin sa.
A wata sanarwar ta daban kuma, wakilin musamman na babban magatakardar MDD a Afghanistan Tadamichi Yamamoto, ya ce tsabar rashin tunani ne ya sanya mayakan Taliban kutsawa cikin otal din, kawai domin kaiwa fararen hula hari.(Saminu)