in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jerin harin bama bamai sun halaka mutane 41 a Afghanistan
2017-12-29 09:53:18 cri

Mutane 41 ne suka mutu, wasu 84 kuma suka jikkata bayan wasu jerin bama bamai sun fashe a cibiyar al'adu dake yammacin Kabul, babban birnin kasar Afghanistan.

Kakakin ma'aikatar lafiya ta kasar Wahid Majroh ya ce, daga cikin wadanda suka mutu sanadiyyar harin ta'addancin na jiya, akwai mata 4 da yara 2, sannan wasu mata 8 na daga cikin wadanda suka jikkata.

Harin ya auku ne da safe bayan 'yan ta'addan sun kai hari kan cibiyar al'adu ta Tebyan dake yankin Dasht-i-Barchi.

Kungiyar IS dai ta dauki alhakin kai harin. ( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China