in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zaftarewar kankara ta hallaka mutane a kalla 50 a gabashin Afghanistan
2017-02-06 09:30:27 cri

A kalla mutane 50 ne suka rasu, kana wasu da dama suka jikkata, bayan da tarin dusar kankara ta zaftare, ta kuma auka kan kauyen Hafsaa dake lardin Nuristan a gabashin kasar Afghanistan.

Rahotanni na cewa, lamarin ya auku ne da tsakar daren jiya Lahadi, kuma akwai fargabar cewa yawan mutanen da bala'in ya shafa na iya karuwa, yayin da mahukunta ke ci gaba da daukar matakai na tono mutane, daga gidaje da dama da kamkarar ta binne.

Wani jami'in yankin ya ce, kankarar ta toshe titunan dake zuwa yankin, ana kuma fama da wahalhalu masu yawa, a kokarin da ake yi na kaiwa ga yankin da wannan lamari ya auku domin aikin ceto.

Ya zuwa yanzu dai kimanin mutane 90 ne suka rasa rayukan su cikin kwanaki 3 da suka gabata, sakamakon zubar dusar kankara, da tsanantar yanayin sanyi a sassan kasar ta Afghanistan. Kaza lika kankara ta lalata sama da gidaje 200 a yankunan dake tsaunukan kasar.

Cikin sa'o'i 24 da suka gabata, jami'an hukumar tsaro da yaki da bala'u ta kasar, sun ceto fasinjoji da dama dake cikin wasu motoci 40, wadanda suka makale a kan hanyar dake hada Kabul, da kuma jihar Kandahar dake kudancin kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China