in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare janar na MDD ya yi Allah wadai da harin ta'addanci a Afghanistan
2017-06-01 09:35:30 cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya yi Allah wadai da kakkausar suka game da harin ta'addanci a Kabul, babban birnin kasar Afghanistan, wanda ya yi sanadiyyar hallaka mutane 80, kana wasu mutanen 350 sun samu raunuka.

Wani harin bam mai karfin gaske makare cikin wata mota a unguwar diplomasiyya dake birnin Kabul ya yi sanadiyyar lalata wasu motoci sama da 50 tare da lalata wasu gidaje masu yawa.

Kawo yanzu babu wata kungiya da ta yi ikirarin daukar alhakin kaddamar da harin.

Babban sakataren MDD ta bakin kakakinsa Stephane Dujarric, ya shedawa 'yan jaridu cewa, ya yi Allah wadai da wannan hari, sannan ya jaddada aniyar yaki da ta'addanci da ayyukan masu tsattsauran ra'ayi.

Dujarric ya kara da cewa, kaddamar da hare hare kan fararen hula mummunan laifi ne da ya saba dokokin hakkin dan adam na kasa da kasa, kana ya bayyana cewa, ya zama tilas a binciko wadanda suka kaddamar da wannan harin domin su gurfana a gaban shari'a.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China