in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta nuna damuwa game da sukar da Amurka ta yi mata don gane da kare hakkin bil Adama
2018-01-22 09:49:50 cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta nuna rashin jin dadi, game da sukar da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya yiwa Sudan, don gane da kare hakkokin bil Adama.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar a jiya Lahadi, ta ce Amurka ta gaza fahimtar irin ci gaba da aka samu a fannonin kare martabar bil Adama, da ikon furta albarkacin baki a kasar ta Sudan.

Kaza lika sanarwar ta ce, a zahiri take cewa, yanzu haka akwai jaridu kusan 20 da ke fita duk rana a kasar Sudan, wadan da ke kunshe da ra'ayoyin siyasa mabanbanta, masu dauke da ra'ayoyin 'yan kasar na kashin kan su. An kuma hore damar hakan ga kowa, muddin dai matakin bai keta hurumin tsarin mulkin kasar ba.

A ranar Juma'a ne dai ma'aikatar harkokin wajen Amurka, ta yi Allah wadai da tsare wasu 'yan jarida a kasar ta Sudan, bayan da aka zarge su da dauko labarai game da zanga zangar da ta biyo bayan hauhawar farashin kayan masarufi da aka yi a ranar Laraba, matakin da ya sanya Amurkan ke ganin har yanzu, batun kare hakkin bil Adama na fuskantar babban kalubale a kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China