in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangarori a Sudan ta kudu na zargin juna da wargaza yarjejeniyar zaman lafiya
2017-12-28 09:31:39 cri

Rundunar sojin kasar Sudan ta kudu da babbar kungiyar 'yan tawayen kasar suna zargin junan su da yunkurin lalata yarjejeniyar zaman lafiyar kasar wadda ta fara aiki a ranar 24 ga watan Disamba.

A ranar Alhamis ta makon jiya ne, aka kulla yarjejeniyar tsakaita bude wuta tsakanin gwamnatin Sudan ta kudun da kungiyoyin 'yan tawayen kasar da dama, wadda kungiyar raya yankin gabashin Afrika IGAD ta shiga tsakani.

Yarjejeniyar ta bukaci bangarorin da ba sa ga maciji da juna a kasar, da su dakatar da amfani da karfin soji, kana su sake dukkan fursunonin siyasa da suke tsare da su.

Lul Ruai Koang, mai magana da yawun rundunar sojin 'yantar da al'ummar Sudan ta (SPLA), ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Laraba cewa, 'yan tawayen dake biyayya ga tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar ne, suka kaddamar da hare hare a yankunan dake karkashin ikon dakarun gwamnati a arewaci da kudancin kasar tsakanin ranakun 22-25 ga watan Disamba.

Lam Paul Gabriel, mataimakin kakakin kungiyar 'yan tawayen SPLA-IO, a nasa bangaren, ya zargi dakarun gwamnati da laifin kaddamar da hare hare kan sansanin 'yan tawayen a sassa daban daban na kasar.

Dukkanin bangarorin biyu dai, sun sha saba yarjejeniyoyin zaman lafiya da aka kulla a lokuta daban daban, tun bayan barkewar yakin basasar kasar shekaru 4 da suka gabata.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China