in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan da Habasha sun amince su tura dakarun hadin gwiwa kan iyakokinsu
2018-01-17 10:32:06 cri

Kasashen Sudan da Habasha sun amince su tura dakarun tsaron hadin gwiwa zuwa kan iyakokinsu, a wani mataki na hada aukuwar duk wani tashin hankali tsakanin kasashen biyu.

A jiya ne dai aka kammala wani taron karawa juna sani game da bunkasa tsaron kan iyakoki tsakanin jihar Blue Nile ta Sudan da yankin Benishangul-Gumuz na kasar Habasha a birnin Damazin, babban birnin jihar ta Blue Nile.

Wata sanarwa da gwamnan Blue Nile Hussein Yassim Hamad ya rabawa manema labarai, ta ce, sassan biyu sun amince su kare iyakokin nasu, domin baiwa sauran kwamitocin da aka kafa damar gudanar da ayyukansu.

Ya kuma nanata kudurin Sudan na tabbatar da zaman lafiya da kare babbar madatsar ruwan nan ta Habasha dake kusa da kan iyakar kasar ta Sudan.

A nasa bangaren gwamnan yankin Benishangul-Gumuz, Al-Shazali Hassan ya lashi takwabin kawo karshen duk wani abin da zai kawo tashin hankali a Sudan, kamar ayyukan fasa kwaurin kayayyaki da makamai a kan iyakokin kasashen biyu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China