in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aljeriya da Najeriya za su dauki matsaya iri guda a matakan tarayyar Afrika da MDD
2018-01-21 12:40:06 cri
Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama, ya bayyana cewa kasashen Aljeriya da Najeriya sun amince za su dauki matsaya iri guda a matakai na kungiyar tarayyar Afrika AU da dana MDD.

Bayan wata ganawar da ya gudanar da takwaransa na Aljeriya Abdelkader Messahel, ministan harkomin wajen Najeriyar ya fadawa 'yan jaridu cewa, ganawar tasu ta mayar da hankali ne game da sha'anin tattaunawar siyasa tsakanin kasashen biyu a matakin shiyya da kuma na kasa da kasa, da nufi cimma matsaya iri guda tsakanin bangarorin biyu a mataki na tarayyar Afrika da MDD.

Ya ce, kasashen Aljeriya da Najeriya sun sha alwashin zurfafa hadin gwiwarsu a fannoni da dama, musamman a fannonin tabbatar da tsaro da yaki da ayyukan ta'addanci, da samar da ingantaccen shugabanci, da bunkasa tattalin arziki da ababen more rayuwa.

A fannin tattalin arziki, babban jami'in diplomasiyyar Najeriyar ya bayyana cewa, sun tattauna game da wasu muhimman ayyukan raya ci gaba na kasashen biyu, da suka hada da aikin shimfida bututun iskar gas, da gina titin mota da zai hade kasashen kudu da hamadar Sahara, da hanyoyin sadarwa wadanda ake sa ran za su hade kasashen biyu.

Onyeama ya ce ana fata wadannan ayyuka za su kara karfafa mu'amala da kuma bunkasa ci gaban nahiyar, a matsayin wani bangare na bunkasa ci gaban Afrika baki daya. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China