Mataimakiyar firayministar ta bayyana haka ne lokacin da take ganawa da ministar harkokin wajen Afrika ta Kudu Maite Nkoana-Mashabane.
Ta ce kaddamar da wannan tsari a zo a kan gaba, wadda ta ce zai kara karfafa dangantaka dake tsakanin kasar Sin da Afrika ta kudu, ta hanyar kara samun goyon baya daga al'ummominsu.
Liu Yandong ta yi imanin cewa, shirin zai bada damar jin amon kasashen Afrika da sauran kasashe masu tasowa ga sauran sassan duniya, da kara bunkasa hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da Afrika ta kudu da ma nahiyar Afrika baki daya. (Fa'iza Mustapha)