Yayin ganawarsa da jakadan Afrika ta Kudu a Nijeriya Lulu Mnguni, Ministan yada labarai da al'adu na kasar Lai Mohammed, ya ce shirin ya dace da kudurin shugaban kasar Muhammadu Buhari, kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da nufin kawo karshen kyamar baki.
Lai Muhammed ya kuma bayyana Nijeriya da Afrika ta Kudu a matsayin 'yan uwan juna, yana mai cewa, duk da rashin fahimta da su kan samu a wasu lokuta, kasashen biyu na da daddadiyar dangantaka.
A cewar gwamnatin Nijeriya, sama da 'yan Nijeriya 100 ne suka mutu ko suka jikkata yayin zanga-zangar kin jinin baki da ya barke a fadin Afrika ta Kudu a shekarar 2013.
Ministan ya bayyana shirin a matsayin ingantacciyar hanyar da za ta kawo karshen kyamar baki da karfafa fahimta tsakanin kasashen biyu. ( Fa'iza Mustapha)