in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan malaria tsakanin kananan yara a Ghana ya ragu zuwa kashi 21
2017-07-28 10:17:05 cri

Binciken tasirin cutar zazzabin cizon sauro wato malaria a kasar Ghana, ya ce kasar ta samu gagarumar nasara wajen rage yawan cutar a tsakanin yara kanana masu watanni 6 zuwa 59.

Binciken da hukumar kididdiga ta kasar ta aiwatar da hadin gwiwa shirin takaita cutar malaria da hukumar lafiya ta kasar, ya lura cewa, yawan cutar tsakanin yara kanana ya ragu sosai da kashi 6, inda ya koma kashi 21 cikin 100 a bara, daga kashi 27 da ya kansance cikin shekarar 2014.

Mukaddashin babban jami'in kididdiga na kasar Baah Wadieh, ya ce har yanzu ana bukatar kara himmantuwa don samun dorewar raguwar cutar.

Binciken ya nuna cewa, an samu nasarar ne bisa matakan kariya da aka dauka, ciki har da mallakar gidajen sauro masu feshin magani, wanda ya rubanya na shekaru 8 da suka gabata. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China