in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Amurka sun yi hira ta wayar tarho
2018-01-16 14:32:26 cri
Yau Talata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump ta wayar tarho.

Yayin zantawar, shugaba Xi ya bayyana cewa, ya kamata kasar Sin da Amurka su mutunta juna, da mai da hankali kan karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma warware sabanin dake tsakaninsu, da kare muradun juna, ta yadda za a raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu cikin yanayi mai kyau.

A nasa bangare, shugaba Trump ya nuna cewa, yana son karfafa mu'amalar dake tsakanin manyan jami'ai da al'ummomin kasashen biyu, domin habaka hadin gwiwar kasashen biyu a fannoni daban daban, da kuma warware matsalolin tattalin arziki da ciniki da kasashen biyu suke fuskanta yadda ya kamata, ta yadda za a ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba.

Haka kuma, shugaba Xi Jinping ya yi bayani game da yanayin da ake ciki a zirin Koriya, yana mai cewa, kasar Sin tana son hada kai da kasar Amurka da ma sauran kasashen duniya domin warware matsalar zirin Koriya.

Shi ma a nasa bangare, shugaba Trump ya ce, kasarsa tana mai da hankali kan muhimmiyar rawar da kasar Sin take takawa wajen warware batun zirin Koriya, a don haka, kasar Amurka tana son karfafa mu'amala da kasar Sin kan wannan batu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China