Shafin Intanet na gwamnatin kasar Equatorial Guinea ya bayar da labari jiya Alhamis 11 ga wata, cewa ministan harkokin wajen kasar Agapito Mba Mkuy ya bayyana a Laraba cewa, ko shakka babu, yunkurin juyin mulkin da aka murkushe a kasar a karshen watan jiya, wani lamari ne na ta'addanci da aka kitsa daga ketare.
A cewarsa, ya zuwa yanzu dai gwamnatin kasar ta riga ta kama 'yan ta'adda 27, kuma kura ta riga ta lafa, sai dai kuma dumbin 'yan ta'addan suka tsere, yayin da wasun su ke samun mafaka a sassan gandun dajin da ke kan iyakar kasar ta Equatorial Guinea da kasashe makwabtan ta.(Kande Gao)