in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Equatorial Guinea ta fidda sakamakon zaben 'yan majalisar dokokin kasar
2017-11-19 13:39:16 cri
A daren ranar 17 ga wata, kwamitin kula da harkokin zabe na kasar Equatorial Guinea ya gabatar da sakamakon zaben 'yan majalisar dokokin kasar, inda mambobin kawancen jam'iyyun hadin gwiwa dake karkashin jagoranci na jam'iyya mai mulkin kasar, wato jam'iyyar dimokuradiyya ne suka lashe galibin kujeru a majalisar dokokin kasar.

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, jam'iyyar dimokuradiyya da sauran jam'iyyu guda 14 wadanda suke cikin kawancen jam'iyyun hadin gwiwa sun lashe kujeru 99 daga cikin kujeru guda 100 na majalisar wakilan kasar, a waje guda kuma, sun lashe dukkan kujeru 55 na majalisar dattawan kasar, wadanda jama'ar kasa suka zaba da kansu kai tsaye. Kana, jam'iyyar adawa ta sabbin al'ummomi ta samu kujera daya ne tak a majalisar wakilan kasar.

A ranar 12 ga wata ne aka gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin kasar Equatorial Guinea, kuma, bisa kididdigar da gwamnatin kasar ta yi, an ce, mutane sama da dubu 320 ne suka yi rajista a wannan zabe, kuma dubu 270 daga cikinsu sun jefa kuri'u a zaben na wannan karo, adadin da ya kai kashi 84 bisa dari na yawan wadanda suka yi rajistar.

Shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, shi ne shugaban jam'iyyar dimokuradiyya mai mulkin kasar, kuma tun lokacin da aka fara bin tsarin mulki na jam'iyyu da dama a shekarar 1991, ya zuwa yanzu, jam'iyyar dimokuradiyya ce ke jan ragamar shugabancin kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China