Masharhanta na ganin cewa, kawancen jam'iyyun siyasa dake karkashin jagorancin jam'iyyar demokuradiyya ta Equatorial Guinea, za ta ci gaba da samun rinjayen kujeru. Shugaban kasar na yanzu, Obiang Nguema Mbasogo, shi ne mutumin da ya kafa jam'iyyar demokuradiyya, kana shugban jam'iyyar na yanzu. Tun daga shekara ta 1991 har zuwa yanzu, jam'iyyar demokuradiyya ita ce jam'iyya mai mulki a Jamhuriyar Equatorial Guinea.(Murtala Zhang)