Sanarwar ta bayyana cewa, a ranar 24 ga watan Disamban bara ma, wasu sojojin haya sun shigo biranen Mongomo, Malabo da Bata na kasar Equatorial Guinea inda suka yi yunkurin kaiwa shugaban kasar Teodoro Obiang Nguema Mbasogo hari a lokacin da ke mahaifarsa ta Mongomo. 'Yan jam'iyyar adawa masu tsattsauran ra'ayi sun yi hayar wadannan sojoji ne, tare da samun goyon bayan wasu kasashen waje.
Sanarwar ta kara da cewa, yanzu haka gwamnatin kasar ta hada kai da hukumomin tsaron kasar Kamru sun kama yawancin mutanen dake da hannu a wannan lamari. (Zainab)