in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gano 'yan Najeriya sama da dubu 2 a wasu sansanonin Libya
2017-12-06 09:29:19 cri

Gwamnatin Najeriya ta ce, ta gano 'yan kasarsa guda 2,778 da ake tsare da su a wasu sansanonin da ake garkame da bakin haure a kasar Libya.

Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta rabawa manema labarai, ta ce, jami'an ofishin jakadancin Najeriya dake Libya ne su ka yi nasarar gano su lokacin da suka ziyarar sansanonin da ake tsare da irin wadannan bakin haure a kasar ta Libya, kuma nan ba da dadewa ba za a dawo da su gida bayan sun samu dukkan takardun tafiye-tafiye da ake bukata na barin kasar.

Kimanin 'yan Najeriya 250 ne suka isa gida a jiya Talata daga kasar ta Libya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China