in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin daga tutar kasar Sin a ranar farko ta watan Janairun shekarar 2018 a Beijing
2018-01-01 12:23:18 cri

A sanyin safiyar ranar farko ga watan Janairun shekarar 2018, an yi bikin daga tutar kasar Sin a babban filin Tian'anmen dake tsakiyar birnin Beijing, hedkwatar kasar.

Wannan ne karo na farko da kungiyar sojoji masu faretin maraba da baki da kungiyar kide-kide ta rundunar sojan kasar Sin suka sauke wannan nauyin dake bisa wuyansu cikin hadin gwiwa, bayan da rundunar PLA ta fara sauke nauyin tsaron tutar kasar.

Dubban gwamman al'umma daga sassa daban daban na kasar Sin ne suka taru a babban filin na Tian'anmen, don ganin yadda sojojin kasar Sin za su daga tutar kasar a karo na farko a sabuwar shekarar ta 2018.

Tun daga ranar farko ta watan Janairun bana, za a samu sauye-sauye kan bikin daga tutar kasar Sin a babban filin Tian'anmen. Inda a rana ta farko ta ko wane wata, sojoji 96 masu faretin maraba da baki za su shiga aikin daga tutar kasar. A sauran lokuta kuma, sojoji 66 ne za su shiga aikin. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China