in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNICEF ta bukaci kasashen Afrika da su kula da lafiyar jarirai sabbin haihuwa
2018-01-02 10:53:00 cri
Hukumar tallafawa ilmin kananan yara ta MDD (UNICEF), ta bukaci kasashen Afrika da su tabbatar da ba da kyakkyawar kulawa ga rayuwar jarirai sabbin haihuwa a kwanakin farko na haihuwarsu.

A wata sanarwar data fitar a Nairobi, UNICEF ta ce, kimanin jarirai 48,000 za'a haifa a gabashi da kudancin Afrika cikin wannan sabuwar shekara.

Leila Pakkala, daraktar UNICEF ta shiyyar gabashi da kudancin Afrika, ta bayyana cewa, jariran da za'a haifa a gabashi da kudancin Afrika zasu kasance kashi 12 bisa 100 na adadin jariran 386,000 da za'a haifa a duniya baki daya.

A cewar UNICEF, kashi 58 bisa 100 na wadan nan jariran za'a haife su ne a kasashe 5 dake shiyyar, an yi hasashen za'a haifi mafi yawan jariran cikin sabuwar shekarar ne a kasar Habasha.

UNICEF ta ce, kasashen yankin hamadar Afrika sun dauki kashi 38 bisa 100 na yawan mutuwar jarirai da aka samu a shekarar 2016.

Kididdiga ta nuna cewa, kusan jarirai 2,600 da suke mutuwa a duniya, suna mutuwar ne a cikin sa'o'i 24 da haihuwarsu, a kullum a cikin shekarar ta 2016, inji UNICEF.

Daga cikin wadannan yaran, kashi 80 bisa 100 na mutuwar jariran yana faruwa ne sakamakon wasu matsaloli wadanda za'a iya kauce musu da suka hada da zubewar ciki, da nakuda mai tsawo a lokacin haihuwa, da kuma wasu nau'ikan cututtuka kamar su cutuka da suka shafi jini da ciwon namoniya.

A cewar hukumar ta UNICEF, duk da cewar an dan samu cigaba wajen kula da jarirai a nahiyar, amma har yanzu matsalar mace macen kananan yara tana da girma, kuma ta kasance a matsayin babban kalubale wanda ke bukatar a kara kaimi wajen dakile ta a kasashen na Afrika, musamman don cimma nasarar magance matsalar mutuwar jarirai da kula da lafiyarsu ta yadda zai yi daidai da mizanin kasa da kasa.

UNICEF ta ce a watan Fabrairu za ta kaddamar da wani shirin inganta lafiyar yara kanana, wanda ya shafi duniya baki daya da nufin samar da yanayin haihuwa da kula da ingancin lafiyar mata da jarirai.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China