Wani rahoton da asusun na UNICEF ya fitar, ya nuna cewa, kasar Liberia ce ta ke kan gaba a wannan matsala,inda kimanin kaso biyu bisa uku na yaran da suka cancanci shiga makarantar firamare a kasar ba sa samun damar zuwa makarantar. Kasar Sudan ta Kudu ce ta biyu da kaso 59 na yaran da ba sa zuwa makarantar firamare, sai kasar Afghanista mai kaso 46 cikin 100,Nijar na da kaso 38, sai kuma Najeriya mai kaso 34 cikin 100 na yaran da ba sa samun damar zuwa makarantar firamare. Sai dai kuma rahaton asusun na Unicef bai ambaci kasashen Somaliya da Syria ba, saboda yake-yaken da ke faruwa a kasashen.
Bayanan na Unicef sun dora alhakin matsalar da ke faruwa a wadannan kasashe ne kan tashe-tashen hankula,matsalar fari,ambaliyar ruwa, girgizar kasa da kangin talauci.
Sai dai kuma, asusun ya ce, yana fargabar cewa,yaran da ke zaune a wadannan kasashe, za su girma ba tare da wata sana'a ko kwarewar da suke bukata don taimakawa ci gaban tattalin arikin kasashensu ba.
Rahotanni na nuna cewa, duk da kiraye-kirayen da ake yi na neman bunkasa bangaren ilimi,har yanzu kaso 31 cikin 100 kawai aka samu.(Ibrahim)