in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban gidan rediyon kasar Sin CRI Wang Gengnian ya gabatar da jawabin murnar sabuwar shekara ta 2018
2018-01-01 10:16:42 cri

A farkon shekarar bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba bayar da wani jawabi a yayin taron dandalin tattalin arzikin duniya da aka gudanar a birnin Davos dake kasar Switzerland, inda ya gabatar da raya makomar dan Adam bai daya. Ban da wannan kuma, an gudanar da taron hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" a watan Mayun bara a nan birnin Beijing, sannan an kira taron shugabannin kasashen kungiyar BRICS a birnin Xiamen na kasar Sin a watan Satumbar bara, an kuma yi taron tattaunawa tsakanin manyan shugabannin jam'iyyar kwaminis ta Sin da na jam'iyyun siyasun kasashen duniya. Duk wadannan sun nuna yadda kasar Sin ta shaida mutuncinta na yin imani da kanta da hakuri da juna da daukar nauyin dake kanta bisa ka'idojin shimfida zaman lafiya da samun bunkasuwa da moriyar juna da bude kofa ga kasashen waje.

A zamanin da muke ciki, ana ganin manyan sauye-sauye dake faruwa a yanayin siyasa na kasa da kasa, kana ana kara kokarin bullo da sabon tsarin tattalin arziki da na siyasa a duniyarmu. A bisa wannan yanayi ne, ya sa zaman lafiya, ci gaba, hadin gwiwa, da samun moriya tare, suka kasance muhimman abubuwan da ake kokarin ganin an samu.

Muna da imanin cewa, mu'amala da musayar ra'ayi su ne hanyoyin da ake bi don samun fahimtar juna, da zurfafa abokantaka. A shekarar da ta gabata, gidan rediyon CRI ya mai da hankali kan wasu manyan ayyukan da suka hada da watsa labarai ta harshen asali, da watsa labarai ga wani wuri ta kafofin watsa labarun wurin, da hada hanyoyin yada labarai daban daban waje guda, da hadin gwiwa da wasu kafofin watsa labaru. Ta wadannan hanyoyi, CRI ya samu ci gaba a kokarinsa na neman zama wata babbar kafar watsa labaru ta zamani, wadda ke da sabbin na'urorin ci gaba daban daban.

1  2  3  4  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China