in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban gidan rediyon kasar Sin CRI Wang Gengnian ya gabatar da jawabin murnar sabuwar shekara ta 2018
2018-01-01 10:16:42 cri

A shekarar 2017, masu sauraronmu kimanin miliyan 95 ne suka yi musayar ra'ayi da mu, kana yawan mutanen da suka ziyarci shafukanmu na sada zumunta na harsuna daban daban ya zarce miliyan 62, yayin da mutanen da suke yin amfani da manhajar mu ta APP sun zarce miliyan 26, jimlolin da suka kafa tarihi.

Mun fahimta cewa, ku abokanmu ne na gaske, saboda duk wani yabon da kuka yi, da ra'ayi da kuka bayyana, da wasikun da kuka rubuto mana, sun nuna yadda kuke goyon bayanmu, da yadda kuke son ganin ci gaban harkokinmu. Don haka, a nan a madadin dukkan ma'aikatan CRI ina muku matukar godiya.

Wani lokaci, a sabuwar shekara, wasu abubuwa masu tarin yawa kan canja. Saboda haka, a cikin wannan sabuwar shekarar 2018, za mu kara kokarin samar da ingantattun bayanai da damu-damuminsu ga abokanmu, da kokarin bullo da karin dandali masu kyau, inda abokanmu za su samu damar sani da fahimtar kasar Sin, gami da daukacin duniyarmu.

Da fatan zumuncin dake tsakaninmu zai dore har abada! Ina sake taya ku murnar sabuwar shekara! Mun gode!


1  2  3  4  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China