in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban gidan rediyon kasar Sin CRI Wang Gengnian ya gabatar da jawabin murnar sabuwar shekara ta 2018
2018-01-01 10:16:42 cri

Yau ce rana ta farko a shekarar 2018, a madadin daukacin ma'aikatan gidan rediyon kasar Sin CRI, shugaban CRI Wang Gengnian yana taya masu sauraro murnar sabuwar shekara ta hanyar rediyo da internet. Wang Gengnian ya bayyana cewa, masu sauraro aminai ne na CRI. Saboda goyon baya da masu sauraro suka nuna masa, CRI yana ta samun ci gaba ba tare da tangarda ba. A sabuwar shekara ta 2018, CRI zai gabatar da karin labarai ko bayanai ko shirye-shirye masu kayatarwa, don samar da wani dandali ga masu sauraronmu wajen kara fahimtar kasar Sin da ma duniya baki daya.

Assalam Alaikum masu sauraro,

A yayin da muke maraba da shigowar sabuwar shekarar 2018, a madadin gidan rediyon kasar Sin CRI kana gidan rediyo da talibijin da internet na kasar Sin CIBN, ina taya ku murnar sabuwar shekara da fatan alheri.

Shekarar 2017 shekara ce mai tarin muhimmanci ga kasar Sin. A shekarar ma, aka gudanar da babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 cikin nasara, wanda ya tsara shirin raya kasar Sin a nan gaba, da samar da shirin kasar Sin game da tafiyar da harkokin duniya. Kamar yadda Franka Gulin wani mai bibiyar shafin Intanet na CRI ya fadi cewa, taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 wani muhimmin batu ne ga kasar Sin, kana muhimmin batu ne dake jawo hankalin kasa da kasa. Idan aka ce Sin ta cimma wasu nasarori na tarihi cikin shekaru biyar da suka gabata, to a nan gaba Sin za ta kafa wani sabon babi mai karin haske a tarihi.

1  2  3  4  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China