in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban gidan rediyon kasar Sin CRI Wang Gengnian ya gabatar da jawabin murnar sabuwar shekara ta 2018
2018-01-01 10:16:42 cri

Yayin da gidan rediyon kasar Sin na CRI yake raya fasahohin da suka hada da watsa labarai ta sauti da kuma bidiyo, da shafin Intanet, da jarida, CRI yana kuma ba da muhimmanci matuka kan raya sabbin fasahohin watsa labarai masu nasaba da wayar salula, don nuna wa abokanmu ainihin yadda kasar Sin take, da kuma fannonin daban-daban na kasar.

Mun yi kokarin samar da wasu kananan fina-finan bidiyo, da bayanai masu kunshe da hotuna, don kayatar da abubuwan da muke watsawa, da hanyoyin da ake bi wajen watsa su, ta yadda za su dace da bukatun abokanmu.

Ban da haka kuma, CRI na kokarin hadin gwiwa da takwarorinsa na kasashen waje, don neman kulla hulda da karin abokai masu sauraro da kallonmu, ta yadda za ta zama wata kafar watsa labarai dake kusa da su, wadda ke kara samar musu da bayanai game da abubuwan dake faruwa a duniya.

Haka zalika, muna kokarin bullo da sabbin hanyoyin karfafa mu'amala tsakanin kasashe daban daban ta fuskar al'adu, inda muke kokarin gabatar da wani shiri na musamman mai taken "Dakin wasan kwaikwayon kasar Sin" wanda za a rika watsawa a gidajen talibijin na kasashe daban daban. Ta hanyar watsa fina-finan kasar Sin da aka fassara su zuwa harsuna daban daban, mun samarwa abokanmu sabuwar damar ganin abubuwan dake faruwa a kasar Sin, da kara fahimtar kasar Sin.

Abokai da aminai, iri ba zai iya fito da tsiro, ya ci gaba da girma ba, idan babu rana, ruwan sama, da kuma tabo ko kasan da za a shuka shi a ciki ba. Haka lamarin yake, idan ba mu samu goyon bayan da kuke nuna mana ba, gidan rediyon CRI ba zai ci gaba cikin sauri ba.

1  2  3  4  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China