in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AMISOM ta yi taro game da yanayin tsaro a Somalia
2017-11-13 10:19:06 cri

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afirka AU da hadin gwiwar MDD dake aiki a Somalia ko AMISOM a takaice, ta gudanar da taron tattaunawa, domin nazartar halin da ake ciki game da sha'anin tsaro a kasar Somalia.

Taron wanda ya samu halartar wakilai daga ma'aikatun gwamnatin kasar, da mambobin kasashe wakilan hukumomin kungiyoyin, da sauran masu ruwa, da tsaki na kasa da kasa, na zuwa ne yayin da gwamnatin Somaliar ke matsa kaimi, wajen kaddamar da hare hare kan dakarun kungiyar Al-Shabaab masu tada kayar baya a kudancin kasar.

Da yake tsokaci game da hakan, wakilin MDD dake Somalia Michael Keating, ya ce ta'addanci shi ne babban kalubale dake haifar da barazana ga tsaro da zaman lafiya a kasar.

Wata sanarwa da ofishin dake tallafawa shirin wanzar da zaman lafiya a Somalia ko UNSOM ya fitar, ta ambato Mr. Keating na cewa, manyan batutuwan da aka mai da hankali kan su, sun hada da zakulo dabarun ci gaba da warware matsaloli a Somalia, da wanzar da ci gaban da aka samu a fannin tsaro.

Keating ya ce, ya zama wajibi a baiwa fannin siyasar kasar kariya, ko a kai ga ci gaba da ginin kasar, da wanzar da zaman lafiya da lumana tsakanin al'ummun ta, da tunkatar sauran matsaloli na zamantakewar al'ummar kasar, masu nasaba da tattalin arziki da siyasa, da kwaskwarima ga kundin dokokin kasa, da samar da guraben ayyukan yi, da kuma kyautata ayyukan samar da hidima.

Jami'in ya kara da cewa, akwai bukatar bullo da dabaru karkashin kulawar gwamnatin Somalia da hadin gwiwar kungiyar AU, wadanda za su taimaka wajen baiwa fararen hula kariya, da hanyoyin shigar da kayayyakin bukatu, tare da bunkasa ayyukan hadin gwiwa, da na karfafa ayyukan rundunonin tsaron kasar a cikin gida.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China