in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNICEF ya yi kira da a kara kokarin hana yaduwar cutar Sida tsakanin matasa
2016-07-19 10:49:25 cri

Asusun kula da kananan yara na MDD (UNICEF) ya yi kira a ranar Talata cewa, har yanzu akwai sauran aiki domin kare kananan yara da matasa daga kamuwa da cutar Sida.

Matasa na ci gaba da mutuwa sakamakon cutar Sida cikin wani yanayi mai tayar da hankali, duk da muhimmin kokarin da aka cimma wajen yaki da wannan annoba ta Sida a duniya a tsawon shekaru goma sha biyar na baya bayan nan, in ji asusun UNICEF a yayin bikin bude dandalin kasa da kasa kan Sida karo na 21, a birnin Durban na kasar Afrika ta Kudu.

Cutar Sida ita ce ta biyu dake dalilin mutuwar yara masu shekaru 10 zuwa 19 a dukkan fadin duniya, kuma cuta ta farko a Afrika, a cewar Anthony Lake, babban darektan UNICEF.

Kokarin rigakafi ya taimaka wajen rage yaduwar Sida da kusan kashi 70 cikin 100 a dukkan fadin duniya tun daga shekarar 2000, musammun ma bisa taimakon aiki hadin gwiwa domin hana yaduwar wannan cuta daga uwa zuwa jariri a cikin kasashen inda cutar ta zama annoba, musammun ma a kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara. Amma duk da haka, adadin mace macen dake nasaba da Sida daga cikin matasa masu shekaru 15 zuwa 19 ya lunka sau biyu tun daga shekarar 2000.

A shekarar 2015, sabbin masu kamuwa da cutar kusan 29 a duk awa guda sun fito daga wannan rukunin shekaru a fadin duniya, in ji UNICEF. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China