in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libya ta yi kira da a kafa cibiyar kula da bakin haure ta kasa da kasa
2017-12-06 09:58:29 cri

Mataimakin firaministan kasar Libya da MDD ke marawa baya Ahmad M'etig ya yi kira da a kafa cibiyar kula da harkokin da suka shafi bakin haure ba bisa ka'ida ba a kasar ta Libya da kuma arewacin Afirka.

M'etig ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke jawabi yayin wani taron karawa juna sani game da masu neman kaura ba bisa ka'ida, taron da hukumar kula da tattalin arziki da jin dadin jama'a ta kasar Libya ta shirya.

Mataimakin firaministan ya kuma jaddada cewa, kafa wannan cibiya, zai taimaka wajen magance matsalolin da kasar ke fuskanta sakamakon bakin hauren dake makalewa a kasar ba bisa ka'ida ba.

A don haka ya yi kira ga kwararru da su mayar da hankali kan wannan batu, domin magance matsalolin da kasar Libyan ka iya fuskanta sakamkon wannan matsala ta bakin haure.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China