in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta karbi bakuncin taron MDD na farko kan bayanan labarin kasa
2017-12-26 10:11:31 cri
Hukumomi a kasar Sin sun ce taron MDD na farko, kan safiyo da tsara taswira, zai gudana a watan Nuwamban badi a yankin Deqing na lardin Zhejiang dake gabashin kasar.

Mataimakin Sakatare Janar na MDD Liu Zhenmin, ya ce mahalarta taron za su yi musayar ra'ayoyi kan nasarorin da aka samu a baya bayan nan game da tsara taswira da safiyo tare da tattauna matakan da za su taimaka wajen cimma muradun ci gaba masu dorewa na MDD.

Liu Zhenmin ya ce ana sa ran yayin taron, za a gabatar da kudurorin da za su magance kalubalen da duniya ke fuskanta a wannnan fanni.

La'akari da samun sabbin fasahohi ciki har da sarrafa tauraron dan adam da kwaikwayon tunanin dan Adam a na'ura mai kwakwalwa, a shekarar 2011, MDD ta kafa wani kwamitin kwararru kan lura da sarrafa bayanan da suka shafi labarin kasa, inda kuma ta kaddamar da wata babbar hukumar kasa da kasa da za ta lura tare da tabbatar da gudanar bangaren.

MDD ce za ta dauki nauyin taron na farko da zai gudana a watan Nuwamban badi, inda hukumar lura da safiyo da tsara taswira da bayanan labarin ilimin kasa da Gwamnatin al'ummar lardin Zhejiang ta kasar Sin za su karbi bakuncinsa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China