in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Italiya na duba yiwuwar shiga yaki da masu safarar bil adama a Nijar
2017-12-26 09:41:13 cri

Firaministan kasar Italiya Paolo Gentiloni, ya ce gwamnatin sa za ta mika bukata ga majalissar dokoki, game da mayar da wasu dakarun kasar dake Iraqi zuwa janhuriyar Nijar, domin yaki da masu safarar bakin haure, da kungiyoyin 'yan ta'adda.

Firaminista Gentiloni ya bayyana hakan ne, cikin sakon kirsimeti da ya gabatarwa dakarun sojojin ruwan kasar, wadanda ke aiki a jirgin ruwan Etna a ranar Lahadi.

Ya ce, batun safarar bil'adama daga yankunan kudu da hamadar Sahara, da Gabas ta Tsakiya zuwa kudancin Turai ta tekun Meditireniya, na cikin muhimman batutuwa da Italiya ke mai da hankali a kai.

Jami'in ya kara da cewa, fatan gwamnatin Italiya shi ne dakile wannan matsala daga tushen ta, musamman ma toshe hanyar da masu aikata wannan laifi ke amfani da ita, ta fasa kwaurin mutane daga yankunan dake fama da tashe tashen hankula a tarayyar Najeriya ta Nijar zuwa tekun Meditireniya.

Firaminista Gentiloni ya kara da cewa, Italiya na kan bakan ta, na kare hakkokin 'yan gudun hijira. Alal misali, yanzu haka tana tallafawa wajen ganin an baiwa 'yan gudun hijira da suka makale a kasar Libiya, damar fita daga sansanonin da ake tsare da su domin komawa kasashen su lami lafiya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China