in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libya da Italiya za su hada hannu wajen yaki da kwararar 'yan ci rani
2017-05-16 10:24:51 cri

Firaministan Libya Fayez Serraj ya gana da ministan harkokin cikin gidan Italiya Marco Minniti jiya Litinin a Tripoli, babban birnin Libya, a wani bangare na inganta dangantakar dake tsakanin kasashensu.

A cewar sashen yada labarai na firaministan, jami'an biyu sun tattauna ne kan batutuwan da suka shafi kasashensu, musammam wadanda suka danganci hadin gwiwarsu kan tsaro.

Abubuwan da suka tattauna sun shafi kwararar 'yan ci rani da kuma horas da jami'an tsaron iyakokin da gabobin ruwa.

Ofishin jakadancin Italiya ya wallafa a shafinsa cewa, Serraj da Minniti sun tattauna kan yaki da kwararar 'yan ci rani. Kuma Italiya da Libya za su aiki kafada da kafada wajen yaki da safarar 'yan ci rani.

Saboda rashin tsaro a yankin, dubban 'yan ci rani ne ke bi ta Libya don tafiya Italiya, inda galibinsu ke nutsewa a tekun Bahr Rum kafin isa Italiyar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China