in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tsaurara matakan tsaro a zagaye na 2 na zaben shugaban Liberiya
2017-12-26 09:30:26 cri

Hukumar 'yan sandan kasar Liberiya ta sanar da cewa, an tsaurara matakan tsaro a duk fadin kasar a yayin da ake gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasar a yau Talata, domin magance duk wata fargabar yiwuwar barkewar tashin hankali a kasar.

Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan kasar Sam Collins, ya sheda wa 'yan jaridu a Monrovia, babban birnin kasar cewa, bayan tattara alkaluman binciken da hukumar 'yan sandan kasar ta yi, ta gano cewa babu wata barazana mai girma na yiwuwar fuskar rikici a zaben.

Za'a fafata a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar ne tsakanin 'dan takarar jam'iyyar adawa ta CDC George Weah, wanda ke kan gaba da yawan kuri'u, da mataimakin shugaban kasar Joseph Boakai na jam'iyya mai mulkin kasar.

Weah, wanda tsohon zakaran wasanni ne na kasar, ya kasance akan gaba da kashi 38.4 cikin 100, yayin da Boakai yake da kashi 28.8 bisa 100.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China