in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyun siyasa a Liberia sun amince da gudanar babban zabe lami lafiya
2017-06-01 10:24:05 cri

Jam'iyyun siyasa a kasar Liberia sun amince da gudanar babban zaben kasar dake tafe nan gaba a karshen shekarar nan lami lafiya.

Daukacin jam'iyyun siyasar kasar masu rajista 22, sun rattaba hannu kan wata takardar amincewa da wannan kuduri, yayin wani taron da suka gudanar a birnin Monrovia, fadar mulkin kasar.

Hukumar zaben kasar ta tabbatar da hakan cikin wata sanarwa, bayan da jam'iyyun siyasar suka mika takardar yarjejeniyar ga ofishin ta.

A cewar shugaban hukumar Jerome George Korkoya, yarjejeniyar na da nufin gani an kammala babban zaben kasar na ranar 10 ga watan Oktoba mai zuwa cikin lumana. Kuma wannan ne karon farko da jam'iyyun kasar suka amince da irin wannan mataki.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China