Shugabar kasar Laberiya, kana kuma shugabar taron shugbannin kasashen kungiyar ECOWAS mai ci, madam Ellen Johnson Sirleaf, ta isa a birnin Niamey na kasar Nijar jiya Alhamis da safe, bisa tsarin wata ziyarar aiki da sada zumanta ta yini guda.
Shugabar Laberiya ta samu babban tarbo daga takwaranta na kasar Nijar Mahamadou Issoufou a filin saukar jiragen saman kasa da kasa na Diori Hamani, tare da sauran shugabannin hukumomin kasa, mambobin gwamnati, 'yan majalisu, da jakadun kasashen waje dake kasar.
Bisa jadawalin wannan ziyara ta yini guda a birnin Niamey, shugabannin biyu sun yi tattaunawa a fadar shugaban kasa, da kuma fadada tattaunawa tsakanin tawagogin kasashen biyu kan huldar dangantakar kasashen biyu da sauran batutuwan dake janyo hankalinsu. (Maman Ada)