in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU da ECOWAS na kokarin kawo karshen sarkakiyar siyasa a Liberia
2017-11-02 09:48:53 cri

Shugabannin kungiyoyin Tarayyar Afrika AU da na ECOWAS mai raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, sun isa Liberia a jiya Laraba, a kokarinsu na kawo karshen yanayin sarkakiya da siyasar Liberia ke ciki.

Da isarsu, shugaban AU Alpha Conde da takwaransa na ECOWAS Faure Gnassingbe, sun gana da jam'iyyun adawa da jam'iyyar Unity mai mulkin kasar da sauran masu ruwa da tsaki, dangane da zagaye na 2 na zaben da za a yi a ranar 7 ga wannan watan.

Siyasar kasar ta shiga wani yanayi mai sarkakiya ne, bayan an yi zargin tafka magudi a zagayen na farko na zaben da aka yi ranar 10 ga watan Oktoba.

A ranar Talata da ta gabata ne kotun kolin kasar ta dakatar da zagaye na biyu na zaben har zuwa lokacin da za ta kammala sauraron karar da jam'iyyu suka shigar gabanta, suna kalubalantar sakamakon zagaye na farko na zaben.

Ana sa ran taron zai kwantar da hankula tare da bukatar jam'iyyun siyasa su tsaya kan yarjejeniyar zaman lafiya da shugabanninsu suka ratabbawa hannu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China