in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Habasha ya yi kira da a karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da wasu kasashe hudu
2017-12-20 09:06:23 cri

Shugaba Mulatu Teshome na kasar Habasha ya yi kira a karfafa hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da wasu kasashen Turai da na Afirka guda hudu.

Shugaba Teshome ya yi wannan kiran ne yayin da ya karbi takardun aikin sabbin jakadun kasashen Sin, Guinea Bissau, Isra'ila, Italiya da Gambia da aka turo kasar ta Habasha, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen kasar ta bayyana cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai.

Teshome ya kuma shaidawa sabbin jakadun cewa, kasarsa za ta mayar da hankali wajen karfafa hadin gwiwa a fannonin kasuwanci da tattalin arziki tsakanin wadannan kasashe, baya ga batun diflomasiya, horas da ma'aikata da kuma kimiyya da fasahar kere-kere.

Yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, sabon jakadan kasar Sin dake kasar Habasha Tan Jian, ya yaba da dangantakar dake wanzuwa tsakanin kasashen biyu, wadda ta kasance abin koyi ga hadin gwiwar kasashen masu tasowa.

Alkaluma na nuna cewa, a cikin shekaru goman da suka gabata, kamfanonin kasar Sin sun zuba jarin da ya kai dala biliyan 4 a kasar Habasha. Kuma darajar cinikayya tsakanin kasashen biyu a shekarar 2015 ta kai dala biliyan 6.37.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China