Babban sakataren MDD Ban Ki Moon ya ajiye furanni domin karrama ma'aikatan da aka kashe a sakamakon harin da 'yan Boko Haram suka kai a ofishinsu dake Abuja, babban birnin kasar a shekaru 4 da suka wuce.
Kafin ya aje furannin dai, Mista Ban ya je Najeriyar ne a wata ziyarar aiki ta kwanaki 2, inda ya sanya hannu a rajistar ta'aziyyar wadanda suka mutu, kuma ya gana da iyalan wasu daga cikin ma'aikatan da harin ya rutsa da su, da wasu manyan jami'an kasashen waje.
A kalla mutane 23 ne suka mutu yayin da wasu 60 suka jikkata a harin da kungiyar Boko haram ta kai kan ofishin MDD dake Abuja a ranar 26 ga watan Agustan shekarar 2011, kuma shi ne harin mafi muni da kungiyar ta taba kaiwa a wani ofishin kasashen waje dake Najeriyar.
Sama da mutane 13,000 ne suka mutu sakamakon hare haren ta'addanci na kungiyar Boko Haram a Najeriyar, batun da Mista Ban ya ce ba za su lamunta ba, kuma dole a kawo karshen ta'addancin ba ma a Najeriya ba, har ma da duniya baki daya domin jama'a su sami walwala
A Litinin din nan ne Ban Ki-moon zai kammala ziyarar tasa bayan ganawa da shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari a fadar gwamnatin wato Villa. (Ahmad Fagam)