in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta jaddada muhimmancin ilimi a aikin wanzar da zaman lafiya
2017-09-08 13:11:33 cri

Shugaban zaman mahawarar MDD game da muhimmancin ilimi Peter Thomson, ya ce mai da hankali ga raya ilimi, mataki ne da zai taimaka wajen dasa akidar son zaman lafiya, da juriya, tare da rungumar dabi'ar hakuri da juna tsakanin al'ummun duniya.

Mr. Thomson wanda ya jagoranci taron na yini guda da ya gudana a birnin New York, ya ce akwai bukatar cusawa yara kanana sha'awar neman ilimi, domin tabbatar da ci gaban su, duba da cewa ilimi zai sa su kauracewa shiga fitintinu, su kuma nuna kauna ga daidaito da martaba juna.

Ya ce ya zama tilas, a koyawa yara kanana dabi'ar juriya, da kaunar daidaito, ta yadda gaba a rayuwa za su kyamaci bin hanyoyi, wadanda ka iya gurbata tarbiyar su.

Ya ce manyan kudurorin ci gaba mai dorewa na MDD, wadanda suka taimaka wajen cimma nasarori a shirin yaki da fatara tun daga shekarar 2015, sun kunshi wanzar da zaman lafiya, da samar da al'ummar duniya mai cike da walwala da karancin fatara.

Baya ga gina al'umma mai wadata ta bai daya, da kare hakkokin bil adama, da biyayya ga dokokin kasa da kasa, kudurorin sun kuma taimaka wajen samar da cibiyoyin bunkasa harkokin gudanarwa tsakanin kasashen duniya.

A nasa bangare babban magatakardar MDD Antonio Guterres, jaddada muhimmancin amfani da matasa ya yi, wajen gina duniya mai cike da zaman lafiya.

Taron na wannan karo dai ya tara wakilan daga kasashe mambobin majalisar, da jami'an ta, da wakilan jam'iyyun gama kai, da 'yan jarida, da sassa masu zaman kan su, tare da sauran masu ruwa da tsaki. An kuma tattauna tare da gabatar da shawarwari, game da batutuwa da suka shafi jigon zaman, da ma hanyoyin aiwatar da shawarwarin da aka gabatar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China