in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta karbi bakuncin taron samar da zaman lafiya tsakanin Palasdinu da Isra'ila
2017-12-16 11:55:45 cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana cewa, kasar Sin za ta karbi bakuncin taron masu yayata tunanin zaman lafiya na Palasdinu da Isra'ila wanda zai gudana tsakanin ranakun 21-22 ga wannan wata na Disamba a nan birnin Beijing.

Lu Kang wanda ya bayyana hakan jiya Jumma'a yayin taron manema labarai da aka saba shiryawa, ya bayyana cewa, mai baiwa shugaban Palasdinawa shawara kan harkokin kasashen waje Nabil Shaath, da Hilik Bar, maitaimakin kakakin majalisar dokokin Isra'ila ne za su jagoranci tawagogin bangarorin biyu a wannan taro. Ana kuma sa ran ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi zai gana da mahalarta taron.

Idan ba a manta ba shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar da wasu shawarwari guda hudu game da batun Palasdinuwa, yayin ganawarsa da shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas a lokacin da ya kawo ziyara kasar Sin cikin watan Yulin wannan shekara.

Shugaba Xi ya jaddada goyon bayan kasar Sin game da kafa kasashe biyu kan batun Palasdinu, kana a kafa kasa mai cin gashin kanta bisa yarjejeniyar kan iyakan da aka shata a shekara 1967, sannan birnin gabashin Kudus ya kasance fadar mulkinta.

Manufar taron dai ita ce, yadda bangarorin biyu za su fito a hanyoyin samar da zaman lafiya a tsakaninsu, tare kuma da bullo wasu sabbin shawarwari kan yadda za a bunkasa shirin samar da zaman lafiyar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China