Wata sanarwa da mahukuntan yankin na Kurdistan suka fitar, ta ce gwamnatin yankin ta amince da fassarar da kotun tarayyar kasar ta yi wa sashe na 1 na kundin tsarin mulkin kasar, game da dakile ballewar yankunan kasar, to sai dai kuma ta ce hakan zai zamo dan ba ne ga burin yankin, na hawa teburin shawarwari, domin warware dukkanin takaddama mai nasaba da salon jagorancin kasar ta Iraqi.
A ranar 6 ga watan Nuwambar nan ne, kotun kolin kasar ta yanke hukunci game da batun neman 'yancin kan yankin na Kurdistan, tana mai tabbatar da cewa, ba wani sashe na kundin da ya amince da ballewar wani yankin kasar ba.
Hakan kuwa ya biyo bayan bukatar fashin baki game da tanaje tanajen kundin tsarin mulkin kasar ne, wanda gwamnatin tarayyar Irakin ta gabatarwa kotun. (Saminu Hassan)