in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta taya shugaba Kenyatta murnar lashe zaben Kenya
2017-08-14 19:46:41 cri
Kasar Sin ta taya shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta murnar lashe babban zaben kasar sa na makon jiya. Mai magana da yawun ma'aikatar wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce kasar Sin na martaba zabin al'ummar Kenya.

Ta ce Sin da Kenya aminan juna ne, kuma 'yan uwa ne dake fatan ci gaba tare, a hannu guda kuma Sin na fatan fadada huldar diflomasiyyar ta da kasar Sin a dukkanin fannoni.

A ranar Juma'a ne dai hukumar zaben kasar Kenya ta IEBC, ta ayyana shugaban kasar Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya lashe zaben kasar na bana. A cewar shugaban hukumar ta IEBC Wafula Chebukati, shugaba Kenyatta ya samu kuri'u miliyan 8.20, adadin da ya kai kaso 54.27 bisa dari na jimillar kuri'un da aka kada. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China