in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi tir da harin bam da aka kai Somalia
2017-10-16 09:56:55 cri

MDD ta yi tir da harin bam da aka kai birnin Mogadishu na Somalia da ya yi sanadin rayuka sama da 230 a ranar Asabar da ta gabata.

Manzon musammam na MDD a Somalia Michael Keating ya ce, abun da ya kamata a ba muhimmanci a yanzu shi ne taimakawa yunkurin hukumomi farfado da al'umma daga alhinin harin, tare da taimakawa wadanda harin ya rutsa da su, musammam wadanda suka jikkata da wadanda suka rasa matsugunansu.

Jami'in ya ce, dole ne dukkan al'ummar kasar su hada kai su yi tir da harin da wannan mummunan ta'addanci

Michael Keating ya ce, shirye-shiryen wanzar da zaman lafiya na MDD da tarayyar Afrika na aiki tare wajen tabbatar da samar da dawwamamen zama lafiya a kasar, inda a yanzu suke taimakawa daukin da gwamnati da hukumomin Mogadishu ke kai wa, ciki har da ba da taimakon kayayyakin aiki da magunguna da likitoci.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China