A cikin rahoton, an ce ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta bayar da rahoton yanayin hakkin bil adama na kasa da kasa na shekarar 2015 a ranar 13 ga wata, inda ta kara nuna ra'ayi ba bisa tushe ba kan yadda hakkin bil adama yake a kasashe daban daban, amma ba ta ce kome ba kan matsaloli masu tsanani da take fuskanta a kan batun.
Rahoton kan yanayin hakkin bil Adama na kasar Amurka na kunshe da kalmomi kimanin dubu 12 da ke shafar batutuwan hakkin jama'a, hakkin tattalin arziki da na al'umma, wariyar launin fata, hakkin mata da kanana yara, da kuma keta hakkin bil adama na sauran kasashe da dai sauransu. (Bilkisu)