in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Habasha ta amince da yarjejeniyar karbo bashi daga Sin don raya kasa
2016-12-28 11:13:14 cri

A jiya Talata majalisar dokokin kasar Habasha ta amince da yarjejeniyoyi 3 game da karbar rancen kudi daga kasar Sin na dala miliyan 380 wanda gwamnatin Sin da bankin Exim na kasar Sin za su samar da kudaden, domin gudanar da muhimman ayyukan gina ababan more rayuwa a kasar ta Habasha.

A cewar shugaban kwamitin kasafin kudi da harkokin kudade na majalisar dokokin Habasha, Birhanu Abebe, kudaden basukan uku da aka amince da su, za a gudanar da muhimman ayyuka ne guda biyu da suka hada da gina hanyoyin mota a Addis Ababa, babban birnin kasar, da kuma aikin tashar samar da hasken lantarki a birnin.

Da yake karin haske ga mambobin majalisar wakilan kasar a jiya Talata, Birhanu ya ce, guda daga cikin ayyukan uku zai lashe dala miliyan 230, wanda shi ne aikin fadada tashar samar da lantarki a birnin na Addis Ababa.

Majalisar dokokin ta kuma amince da yarjejeniyoyi biyu don karbar rance kudaden shimfida titunan mota a babbar birnin kasar wanda zai lashe dala miliyan 102, da kuma dala miliyan 50.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China