in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ICRC: Yawan mutanen da suka mutu a fadan da ya barke a Yemen ya karu zuwa 234
2017-12-06 10:33:46 cri

Kungiyar ba da agaji ta kasa da kasa ta Red Cross(ICRC) mai kula da yankin Gabas ta Tsakiya ta bayyana a jiya Talata cewa, yawan mutanen da suka mutu a fadan da aka kwashe tsawon mako guda ana yi a Sana'a, babban birnin kasar Yemen ya karu zuwa 234, baya ga wasu 400 da suka jikkta, ciki har da wasu mutane 383 da suka ji munanan raunuka.

Darektan shiyya na kungiyar Robert Mardini ya bayyana a shafinsa na sada zumunta na Twitter cewa, ma'aikatan kungiyar na daukar matakan da suka kamata na ganin sun samarwa asibitoci magunguna, mai da sauran muhimman kayayyakin aikin da ake bukata.

A ranar Litinin ne dai, mayakan Houthi suka halaka tsohon shugaban kasar ta Yemen Ali Abdullah Saleh, da 'yan uwansa da babban mai taimaka masa, bayan da kungiyar Houthi da magoya bayan Saleh masu dauke da makamai suka shafe kwanaki uku suna mummunan arangama a titunan birnin Sana'a.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China