in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kerry ya ce kawo karshen rikicin Yemen zai baiwa Saudiyya cikakken tsaro
2016-12-19 10:11:31 cri

Kafar yada labarai ta Al Arabiyya ta rawaito cewa, sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya bayyana a jiya Lahadi cewa, kawo karshen tashin hankali a kasar Yemen zai iya baiwa kasar Saudi Arabiya ingantaccen tsaro.

Da yake jawabi a taron manema labarai tare da takwaransa na kasar Saudiyya Adel Al-Jubeir, mista Kerry, ya bukaci dukkannin bangarorin siyasar kasar da su koma teburin sulhu don warware takaddamar, da kuma cimma matsaya.

Kawo yanzu shirin da MDD ke yi game da magance rikicin Yemen bai kammala ba, kuma har yanzu ana matakin cimma daidaito ne, Kerry ya bayyana cewa, babbar manufar kawo karshen rikicin Yemen ita ce domin a samu warware dambarwar siyasar kasar wanda hakan zai ba da damar gudanar da ayyukan jin kai a kasar.

Babban jami'in diplomasiyyar na Amurkar ya kara da cewa, kasar Amurka kamar Saudiyya ce, tana Allah wadai da yin katsa landan da kasar Iran ke yi game da rikicin kasar Yemen.

Bugu da kari, shi ma Al-Jubeir ya bayyana cewa, duk wata yarjejeniya game da rikicin Yemen ya fi dacewa a mayar da hankali kan batun yarjejeniyar kasashen yankin Gulf, da kuma ta MDD, inda ya bukaci kasashen duniya da su dauki dukkan matakan da suka dace wajen takawa kasar Iran birki game da yin katsalandan a harkokin da suka shafi yankin Gulf.

Mista Kerry ya kuma nanata aniyar Amurka na kawo karshen rikicin Yemen wanda kasar Saudiyya ke jagoranta, wanda zai shiga shekara ta 3 a watan Maris, rikicin ya jefa rayuwan fararen hula cikin matsanancin hali.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China